Littafi Mai Tsarki

M. Had 3:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan abin da yake faruwa a duniyan nan yakan faru ne a cikin lokacin da Allah ya so.

2. Shi yake sa lokacin haihuwa, da lokacin mutuwa,Da lokacin dashe, da lokacin tumɓuke abin da aka dasa,

3. Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa,Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.

4. Shi ne kuma yake sa lokacin yin kuka, da lokacin yin dariya,Da lokacin yin makoki, da lokacin yin murna,

5. Da lokacin warwatsa duwatsu, da lokacin tattarawa,Da lokacin rungumewa, da lokacin da ba a yi.

6. Shi ne kuma yake sa lokacin nema, da lokacin rashi,Da lokacin adanawa, da lokacin zubarwa,

7. Da lokacin ketawa, da lokacin gyarawa,Da lokacin yin shiru, da lokacin magana.

8. Shi ne kuma yake sa lokacin ƙauna, da lokacin ƙiyayya,Da lokacin yaƙi, da lokacin salama.

9. Wace riba mutum zai ci a kan dukan aikinsa?