Littafi Mai Tsarki

M. Had 12:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Hakika, ka tuna da Mahaliccinka kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe, ko tulu ya fashe a bakin rijiya, ko igiya ta tsinke a bakin tafki,

7. sa'an nan turɓaya ta koma ƙasa kamar a dā, ruhu kuma ya koma wurin Allah wanda ya ba da shi.

8. Banza a banza, duk banza ne, in ji Mai Hadishi. Duk a banza ne.

9. Saboda hikimar Mai Hadishi ya koya wa mutane ilimi. Ya auna, ya bincika, ya tsara karin magana da lura sosai.

10. Ya nemi kalmomi, ya rubuta su daidai.

11. Kalmomin mutane masu hikima kamar sanduna suke da makiyaya suke amfani da su, su bi da tumaki.

12. Ya ɗana, ka yi hankali, kada ka zarce waɗannan, gama wallafa littattafai ba shi da iyaka, yawan karatu kuma gajiyar da kai ne!