Littafi Mai Tsarki

M. Had 11:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka jefa kyautarka a baya, ka tsince ta a gaba.

2. Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.

3. Idan gizagizai sun cika da ruwa sukan sheƙar da shi ƙasa. A inda itace ya faɗi, a nan zai kwanta, ko wajen kudu ko arewa.

4. Wanda yake la'akari da iska, ba zai yi shuka ba, wanda kuma yake la'akari da gizagizai, ba zai yi girbi ba.