Littafi Mai Tsarki

Luk 8:53-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

53. Sai suka yi masa dariyar raini, don sun sani ta mutu.

54. Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”

55. Ruhunta kuwa ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci.

56. Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.