Littafi Mai Tsarki

Luk 23:54-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

54. Ran nan kuwa ranar shiri ce, Asabar kuma ta doso.

55. Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa.

56. Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa.Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.