Littafi Mai Tsarki

Luk 20:22-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?”

23. Shi kuwa ya gane makircinsu, ya ce musu,

24. “Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.”

25. Sai ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

26. Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.

27. Sai waɗansu Sadukiyawa suka zo wurinsa (su da suke cewa, ba tashin matattu),

28. suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.

29. To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar na baya ba.

30. Na biyun,

31. da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai, duk bakwai ɗin suka aure ta, suka mutu, ba wanda ya bar ɗa.