Littafi Mai Tsarki

Luk 19:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. ya nemi ganin ko wane ne Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne.

4. Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi.

5. Da Yesu ya iso wurin, ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakka, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.”

6. Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna.

7. Da suka ga haka, duk suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!”

8. Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.”