Littafi Mai Tsarki

Luk 19:27-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”

28. Da Yesu ya faɗi haka, ya yi gaba zuwa Urushalima.

29. Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu,

30. ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi.

31. Kowa ya tambaye ku, ‘Don me kuke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa.’ ”

32. Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu.

33. Suna cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”

34. Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.”

35. Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu.