Littafi Mai Tsarki

Luk 1:68-71 Littafi Mai Tsarki (HAU)

68. “Ubangiji Allahn Isra'ila,A gare shi ne lalle yabo yake tabbata,Domin ya kula, ya yi wa jama'a tasa fansa.

69. Ya ta da Mai Ceto mai iko dominmu,Daga zuriyar baransa Dawuda.

70. Yadda tuntuni ya faɗa ta bakunanAnnabawa nasa tsarkakan nan,

71. Yă cece mu daga abokan gābanmu,Har ma daga dukan maƙiyanmu.