Littafi Mai Tsarki

L. Mah 9:30-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Zebul, shugaban birnin ya ji maganganun Ga'al, ɗan Ebed, sai ya husata.

31. Ya aiki jakadu wurin Abimelek a Aruma, ya ce, “Ga fa Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa sun zo Shekem, suna kutta garin ya tayar maka.

32. Yanzu sai ka tashi, ka zo da dare tare da mutanen da suke tare da kai, ku yi kwanto a cikin saura.

33. Sa'an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga'al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!”

34. Abimelek da mutanen da suke tare da shi kuwa suka tashi da dare suke yi wa Shekem kwanto da ƙungiya huɗu.

35. Ga'al, ɗan Ebed, kuwa ya fita zuwa ƙofar garin daidai lokacin da Abimelek da mutanensa suka tashi daga wurin kwantonsu.

36. Sa'ad da Ga'al ya ga mutanen, ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna zuwa daga kan duwatsu.”Sai Zebul ya ce masa, “Ai, inuwar duwatsu ce kake gani kamar mutane.”

37. Ga'al kuma ya ƙara yin magana, ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa kan hanya, ga kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen oak na masu duba.”

38. Sa'an nan Zebul ya ce masa, “Ina cika bakin nan naka, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa?’ Waɗannan su ne mutanen da ka raina. Fita, ka yaƙe su mana.”

39. Ga'al kuwa ya fita ya yi jagorar shugabannin Shekem, suka yi yaƙi da Abimelek.

40. Abimelek kuwa ya runtumi Ga'al, shi kuwa ya gudu. Mutane da yawa suka ji rauni, ya bi su har bakin ƙofar birnin.

41. Sai Abimelek ya zauna a Aruma. Zebul kuwa ya kori Ga'al da 'yan'uwansa, ya hana su zama a Shekem.

42. Kashegari mutanen Shekem suka tafi saura, sai aka faɗa wa Abimelek.

43. Shi ma ya kwashi mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, suka yi kwanto a saura. Da ya duba, ya ga mutane suna fitowa daga cikin birnin. Ya fāɗa musu, ya karkashe su.

44. Abimelek kuma da ƙungiyar da take tare da shi, suka hanzarta, suka tsare ƙofar birnin. Sauran ƙungiya biyu suka ruga, suka faɗa wa dukan waɗanda suke cikin saura, suka karkashe su.

45. Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri.

46. Da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji labari, suka gudu zuwa hasumiyar gidan Ba'al-berit don su tsira.