Littafi Mai Tsarki

L. Mah 6:39-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Gidiyon kuma ya ce wa Allah, “Ina roƙonka, kada ka yi fushi da ni, bari in ƙara magana sau ɗaya kurum, wato in sāke yin gwaji da ulun. Ina roƙonka ka sa a yi raɓa a ƙasa, amma kada ta taɓa ulun.”

40. Haka kuwa Allah ya yi a daren. Aka yi raɓa a ƙasa, amma ulun yana a bushe.