Littafi Mai Tsarki

L. Mah 6:34-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kan Gidiyon, sai ya busa ƙaho, mutanen Abiyezer suka bi shi.

35. Ya kuma aiki manzanni a ƙasar Manassa duka. Su kuma aka kirawo su su bi shi. Ya kuma aiki manzanni zuwa ga Ashirawa da Zabalunawa, da Naftaliyawa, su kuma suka zo, suka haɗa kai da shi.

36. Sa'an nan Gidiyon ya ce wa Allah, “Ka ce za ka sa ni in ceci Isra'ilawa.

37. To, zan shimfiɗa ulu a masussuka. Idan da safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, sa'an nan zan sani za ka ceci Isra'ilawa ta hannuna kamar yadda ka faɗa.”

38. Haka kuwa ya zama Kashegari Gidiyon ya tashi da sassafe, sai ya matse ulun, ruwan raɓa da ya matse daga ulun kuwa, ya cika ƙwarya.

39. Gidiyon kuma ya ce wa Allah, “Ina roƙonka, kada ka yi fushi da ni, bari in ƙara magana sau ɗaya kurum, wato in sāke yin gwaji da ulun. Ina roƙonka ka sa a yi raɓa a ƙasa, amma kada ta taɓa ulun.”

40. Haka kuwa Allah ya yi a daren. Aka yi raɓa a ƙasa, amma ulun yana a bushe.