Littafi Mai Tsarki

L. Mah 6:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ubangiji ya ce masa, “Tafi da dukan ƙarfinka, ka ceci Isra'ilawa daga Madayanawa. Ni kaina na aike ka.”

15. Gidiyon ya amsa ya ce, “Ubangiji, yaya zan yi in ceci Isra'ilawa? Ga shi, dangina ne mafi ƙanƙanta a kabilar Manassa, ni ne kuma ƙarami a gidanmu.”

16. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Za ka iya, gama zan taimake ka. Za ka muttsuke Madayanawa kamar mutum guda.”

17. Gidiyon kuwa ya ce masa, “Idan ka amince da ni, ka nuna mini alama don in sani kai kake magana da ni.

18. Ina roƙonka, kada ka tashi daga nan, sai na kawo maka hadaya ta abinci.”Ya amsa cewa, “Zan tsaya har ka kawo.”

19. Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak.

20. Mala'ikan Allah kuma ya ce masa, “Ɗauki naman da wainar marar yisti ka sa a kan dutsen nan, sa'an nan ka zuba romon a kai.” Haka kuwa ya yi.