Littafi Mai Tsarki

L. Mah 20:47-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

47. Amma mutum ɗari shida suka juya, suka gudu suka nufi hamada zuwa Dutsen Rimmon inda suka zauna har wata hu:du.

48. Mutanen Isra'ila kuma suka komo, suka fāɗa wa sauran mutanen Biliyaminu. Suka karkashe su, mutane, da dabbobi, da dukan abin da suka iske. Suka ƙone garuruwan wannan yankin ƙasa.