Littafi Mai Tsarki

L. Mah 18:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A kwanakin nan ba sarki a Isra'ila. A wannan lokaci kuwa kabilar Dan suna ta neman yankin ƙasar da za su samu, su zauna. Gama har yanzu ba su sami nasu gādon ƙasa tare da sauran kabilar Isra'ila ba.

2. Sai Danawa suka zaɓi mutum biyar jarumai daga kabilarsu, suka aike su daga Zora da Eshtawol, su tafi leƙen asirin ƙasar, su bincike ta. Suka kuwa tafi zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka sauka a gidan Mika.

3. Sa'ad da suke a gidan Mika ɗin, sai suka ji muryar saurayin nan, Balawe, suka tsaya suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kuma kake yi a nan?”