Littafi Mai Tsarki

L. Mah 14:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba.

7. Sa'an nan ya gangara ya yi zance da budurwar, yana kuwa sonta.

8. Bayan 'yan kwanaki sai ya koma don ya auro ta. Ya ratse don ya duba gawar zakin da ya kashe, sai ya tarar da cincirindon ƙudan zuma, da kuma zuma a cikin gawar zakin, ya yi mamaki.

9. Ya ɗebo zuman a hannunsa, yana tafe yana sha, har ya isa wurin iyayensa, ya ba su, suka sha, amma bai faɗa musu daga cikin gawar zaki ya ɗebo zuman ba.

10. Mahaifinsa ya tafi gidan iyayen yarinyar, Samson kuma ya shirya liyafa a can, gama haka samari sukan yi.

11. Sa'ad da Filistiyawa suka gan shi suka sa samari talatin su zauna tare da shi.

12. Samson kuwa ya ce musu, “Bari in yi muku ka-cici-ka-cici, idan kun faɗa mini amsarsa a kwana bakwai na bikin, to, zan ba ku rigunan lilin talatin da waɗansu riguna talatin na ado.

13. Amma idan kun kāsa ba ni amsar, to, ku ne za ku ba ni rigunan lilin talatin da waɗansu rigunan na ado.”Sai suka ce, “To, faɗi ka-cici-ka-cicin mu ji.”