Littafi Mai Tsarki

L. Mah 1:11-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Daga can suka tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer.

12. Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.”

13. Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi 'yarsa Aksa aure.