Littafi Mai Tsarki

L. Fir 6:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya ba Musa ka'idodin nan.

2. Idan wani mutum ya yi laifi na cin amana gāba da Ubangiji, wato, ya yaudari maƙwabcinsa a kan ajiya, ko jingina, ko ƙwace, ko ya zalunce shi,

3. ko ya yi tsintuwa, amma ya yi mūsu har ya rantse da ƙarya, duk dai irin abubuwan da akan aikata na laifi,

4. sa'ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta,

5. ko kowane abin da ya rantse a kansa da ƙarya. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har ya ƙara da humushin tamanin abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

6. Zai kuwa kai wa firist rago marar lahani daga garken tumaki don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifinsa. Za a kimanta tamanin ragon daidai da tamanin hadaya don laifi.

7. Firist kuwa zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.