Littafi Mai Tsarki

L. Fir 4:17-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sa'an nan ya tsoma yatsansa a cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen.

18. Sai ya ɗiba daga cikin jinin ya shafa wa zankayen bagaden da suke cikin alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, sauran jinin kuwa sai ya zuba a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada.

19. Zai kwashe kitsensa duka, ya ƙone shi bisa bagaden.

20. Sai ya yi da ɗan bijimin kamar yadda ya yi da ɗan bijimi na hadaya don zunubin firist. Ta haka firist zai yi kafara domin jama'a, za a kuwa gafarta musu.

21. Zai kai bijimin a bayan zango, ya ƙone shi kamar yadda ya yi da na farin, gama hadaya ce don zunubin taron jama'ar.

22. Idan shugaba ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.

23. Idan aka sanar da shi zunubin da ya yi, sai ya kawo bunsuru marar lahani don yin hadaya.

24. Zai ɗibiya hannunsa a kan kan bunsurun, ya yanka a wurin da ake yanka hadaya ta ƙonawa a gaban Ubangiji, gama hadaya ce don zunubi.