Littafi Mai Tsarki

L. Fir 3:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare da ƙodojin.

11. Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji.

12. Idan ya kawo akuya don hadayarsa, sai ya miƙa ta a gaban Ubangiji.

13. Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.

14. Sa'an nan mai hadayar zai ba da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa,

15. da ƙodoji biyu, da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama don a miƙa su hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

16. Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone don ya yi ƙanshi mai daɗi. Dukan kitse na Ubangiji ne.

17. Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.