Littafi Mai Tsarki

L. Fir 3:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Idan mutum zai kawo hadayarsa ta salama daga garken shanu, sai ya kawo mace ko namiji marar lahani ga Ubangiji.

2. Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.

3. Daga hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsen da yake rufe da kayan ciki, da wanda yake bisansa,

4. da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare ƙodojin.

5. 'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su ƙone su tare da hadayar ƙonawa da take bisa itacen da yake cikin wutar bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

6. Idan kuwa hadayarsa ta salama ga Ubangiji daga garken tumaki, ko na awaki ce, sai ya ba da dabbar, mace ko namiji, marar lahani.