1. Ubangiji kuma ya ce wa Musa
2. ya umarce Isra'ilawa, su kawo masa tsabtataccen man zaitun da aka matse domin fitilar. Fitilar za ta riƙa ci kullum.
3. Za a ajiye ta a gaban labulen shaida a alfarwa ta sujada. Kullum Haruna zai riƙa lura da ita daga maraice har safiya a gaban Ubangiji. Wannan zai zama muku farilla har abada a dukan zamananku.
4. Kullum sai ya shirya fitilun a bisa alkuki na zinariya tsantsa a gaban Ubangiji.
5. Ɗauki lallausan gari a toya gurasa goma sha biyu. A ki kowace gurasa da humushi biyu na garwar gari.
6. A ajiye su bisa tebur na zinariya tsantsa jeri biyu, shida a kowane jeri.
7. Sai a sa lubban tsantsa a kowane jeri don a haɗa da abincin da za a ƙone domin hadaya ta tunawa ga Ubangiji.