Littafi Mai Tsarki

L. Fir 24:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya ce wa Musa

2. ya umarce Isra'ilawa, su kawo masa tsabtataccen man zaitun da aka matse domin fitilar. Fitilar za ta riƙa ci kullum.

3. Za a ajiye ta a gaban labulen shaida a alfarwa ta sujada. Kullum Haruna zai riƙa lura da ita daga maraice har safiya a gaban Ubangiji. Wannan zai zama muku farilla har abada a dukan zamananku.

4. Kullum sai ya shirya fitilun a bisa alkuki na zinariya tsantsa a gaban Ubangiji.

5. Ɗauki lallausan gari a toya gurasa goma sha biyu. A ki kowace gurasa da humushi biyu na garwar gari.

6. A ajiye su bisa tebur na zinariya tsantsa jeri biyu, shida a kowane jeri.

7. Sai a sa lubban tsantsa a kowane jeri don a haɗa da abincin da za a ƙone domin hadaya ta tunawa ga Ubangiji.

8. Kullum a kowace ranar Asabar, Haruna zai kintsa su a gaban Ubangiji domin Isra'ilawa saboda madawwamin alkawarin.

9. Wannan abinci zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza, za su ci a wuri mai tsarki, tun da yake a gare shi rabo ne mai tsarki daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji. Wannan farilla ce har abada.

10. Ɗan wata mace Ba'isra'iliya wanda mahaifinsa Bamasare ne, ya fita, ya yi faɗa da wani Ba'isra'ile a cikin zangon.