Littafi Mai Tsarki

L. Fir 22:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Firist ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun abubuwan nan da jama'ar Isra'ila suke miƙawa ba,

16. da zai bar mutumin da bai cancanta ya ci ba, wannan zai jawo masa hukunci. Ni ne Ubangiji. Ni na tsarkake hadayun.”

17. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

18. ya yi magana da Haruna da 'ya'yansa maza, da dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Sa'ad da duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune a Isra'ila, ya kawo hadaya ta ƙonawa, ko ta wa'adi ce, ko ta yardar rai, dole ne dabbar ta zama marar lahani.

19. Dabbar ta kasance namiji marar lahani idan ana so ta karɓu.

20. Kada ku yi hadaya da abin da yake da lahani, gama Ubangiji ba zai karɓa ba.

21. Idan kuwa wani ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji don cika wa'adi, ko don hadaya ta yardar rai, daga cikin garken shanu, ko na tumaki, da na awaki, sai ya zama cikakke, marar lahani, don ya karɓu.

22. Dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko mai gundumi, ko mai ɗiga, ko mai susa, ko mai kirci, kada ku miƙa wa Ubangiji, kada kuma ku yi hadaya ta ƙonawa a bagaden Ubangiji da su.

23. Kwa iya ba da dabba, marar cikakkiyar halitta don hadaya ta yardar rai, amma ba za ku bayar don hadaya ta cika wa'adi ba, ba za a karɓa ba.

24. Kowace dabba kuma da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa, ba za ku miƙa ta hadaya ga Ubangiji ba, ba kuwa za ku yi hadaya da ita a ƙasarku ba.