Littafi Mai Tsarki

L. Fir 20:1-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya faɗa wa Musa,

2. ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu.

3. Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki.

4. Idan kuwa mutanen ƙasar ba su kashe mutumin nan, wanda ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa ba,

5. ni kaina zan yi gāba da mutumin nan da iyalinsa, da waɗanda suka yarda suka bi Molek tare da shi. Ba zan ƙara ce da su mutanena ba.

6. “Duk wanda yake sha'ani da masu mabiya, ko da bokaye zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa.

7. Sai ku kiyaye kanku da tsarki, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

8. Ku kuma kiyaye dokokina, ku aikata su, gama ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.

9. “Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.

10. “Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar.

11. Mutumin kuma da ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa ke nan, su biyu ɗin za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.

12. Duk wanda ya kwana da matar ɗansa, za a kashe su duka biyu ɗin, gama sun yi abin da yake haram. Alhakin jininsu yana wuyansu.

13. Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.

14. Duk mutumin da ya auri 'ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku.

15. Idan mutum ya kwana da dabba, sai a kashe shi, a kuma kashe dabbar.

16. In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu.

17. “Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu.

18. Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki.

19. “Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi.