Littafi Mai Tsarki

L. Fir 17:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Gama ran nama yana cikin jinin, Ubangiji kuwa ya ba su shi a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara, gama da jini ake kafara saboda akwai rai a cikinsa.

12. Saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, kada wani daga cikinsu, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, ya ci jini.

13. Idan kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya tafi farauta, ya kama nama, ko tsuntsu da ake ci, sai ya zub da jininsa, ya rufe da ƙasa.

14. Gama ran dukan nama yana cikin jininsa, saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, faufau ba za su ci jinin kowace dabba ba, gama ran kowace dabba yana cikin jininta. Duk wanda kuwa ya ci shi, za a raba shi da jama'a.

15. Duk wanda ya ci mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, ko shi Ba'isra'ile ne, ko baƙo ne, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, ya ƙazantu har maraice, sa'an nan zai tsarkaka.

16. Amma idan bai wanke su ba, bai kuwa yi wanka ba, alhakinsa yana kansa.