1. Ubangiji ya umarce Musa,
2. ya faɗa wa Haruna da 'ya'yansa maza, da dukan mutanen Isra'ila waɗannan ka'idodi.
3. Idan Ba'isra'ile ya yanka sa, ko ɗan rago, ko akuya a cikin zango, ko a bayan zango,
4. bai kuwa kawo shi a ƙofar alfarwa ta sujada don ya miƙa shi sadaka ga Ubangiji a gaban alfarwa ta sujada ba, alhakin jinin da ya zubar yana bisa kansa, za a fitar da wannan mutum daga cikin jama'arsa.
5. Manufar wannan umarni ce domin Isra'ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji.