Littafi Mai Tsarki

L. Fir 14:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ba Musa

2. waɗannan ka'idodi da za a bi a ranar tsarkakewar mai kuturta. Sai a kawo shi ga firist.

3. Firist ɗin zai fita zuwa bayan zango ya dudduba shi. Idan kuturun ya warke daga cutar kuturtar,

4. firist ɗin zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya domin aikin tsarkakewa.

5. Sai firist ya umarta a yanka tsuntsu ɗaya a kaskon da yake cike da ruwa mai gudu.

6. Ya kuma ɗauki ɗayan tsuntsu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon.

7. Sai ya yayyafa jinin sau bakwai a kan wanda za a tsarkake daga kuturtar, sa'an nan ya hurta, cewa, mutumin ya tsarkaka, ya kuma saki tsuntsu mai ran ya tafi cikin saura.

8. Shi kuwa wanda za a tsarkake, sai ya wanke tufafinsa, ya aske dukan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. Bayan wannan zai shiga zango, amma kada ya shiga cikin alfarwarsa har kwana bakwai.

9. A kan rana ta bakwai zai aske dukan gashin kansa, da gemunsa, da gashin girarsa, da duk gashin jikinsa. Sai kuma ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka.

10. A rana ta takwas zai kawo 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da hadaya ta gari rabin garwar gari mai laushi karɓaɓɓe da man zaitun, da rabin moɗa na mai.