Littafi Mai Tsarki

L. Fir 13:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi.

2. Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci.

3. Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne.

4. Amma idan tabon fari ne, zurfinsa kuwa bai zarce fatar ba, gashin kuma da yake cikinsa bai rikiɗa ya zama fari ba, sai firist ya kulle mai ciwon har kwana bakwai.