Littafi Mai Tsarki

L. Fir 11:21-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. sai dai waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.

22. Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu.

23. Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, sun a kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.

24. Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har faɗuwar rana.

25. Duk wanda kuma ya ɗauki mushensu dole ne ya wanke tufafinsa, amma zai ƙazantu har zuwa maraice.

26. Kowace dabba wadda ba ta da rababben kofato, ba ta kuma tuƙa, haram ce a gare ku. Duk wanda ya taɓa su zai ƙazantu.

27. Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice.

28. Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice.

29. Waɗannan ƙananan dabbobin da suke rarrafe a ƙasa haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,

30. da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

31. Duk wanda ya taɓa su ko ya taɓa mushensu, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice.

32. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa'an nan zai tsarkaka.

33. Idan wani daga cikinsu ya fāɗa cikin kasko, to, kaskon da abin da yake cikinsa za su ƙazantu, sai a fasa kaskon.