Littafi Mai Tsarki

K. Mag 30:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne maganar Agur ɗan Yake, da ya yi wa Etiyel da Yukal,

2. “Hakika wautata ta sa na zama kamar dabba ba mutum ba,Ba ni kuwa da fahimi irin na mutum.

3. Ban koyi hikima ba,Ban kuwa san kome game da Allah ba.

4. Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko?Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa?Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa?Wa kuma ya kafa iyakar duniya?Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa?Hakika ka sani!

5. “Kowace maganar Allah takan tabbata. Shi garkuwa ne ga waɗanda suke fakewa a wurinsa.

6. Kada ka yi ƙari a kan maganarsa, don kada ya tsauta maka, a kuma bayyana kai maƙaryaci ne.”