Littafi Mai Tsarki

K. Mag 25:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sa'ad da kake tsaye a gaban sarki, kada ka nuna kai wani abu ne, kana kai kanka inda Allah bai kai ka ba.

7. Gara a roƙe ka ka hau zuwa babban matsayi, da a faɗa maka ka ba da wurin da kake ga wanda ya fi ka maƙami.

8. Kada ka yi garajen kai ƙara a majalisa. Idan wani mashaidi ya nuna kai kake da kuskure, me za ka yi?

9. Idan kai da maƙwabcinka kun saɓa, ku daidaita a tsakaninku, kada a tona asiri.

10. Mai yiwuwa ne wani ya ji ya zarge ku, ba za ku taɓa rabuwa da wannan kunya ba.

11. Manufar da aka bayyana sosai kamar zubin zinariya take wanda aka yi a kan azurfa.