Littafi Mai Tsarki

K. Mag 25:3-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ba ku taɓa sanin abin da sarki yake tunani ba, gama tunaninsa sun fi ƙarfinmu. Kamar nisan sararin sama suke ko zurfafan teku.

4. Ka tace azurfa, gwani kuwa zai yi wani kyakkyawan abu da ita.

5. A kawar da mugayen mashawarta daga gaban sarki, hukumarsa za ta shahara a kan adalci.

6. Sa'ad da kake tsaye a gaban sarki, kada ka nuna kai wani abu ne, kana kai kanka inda Allah bai kai ka ba.

7. Gara a roƙe ka ka hau zuwa babban matsayi, da a faɗa maka ka ba da wurin da kake ga wanda ya fi ka maƙami.

8. Kada ka yi garajen kai ƙara a majalisa. Idan wani mashaidi ya nuna kai kake da kuskure, me za ka yi?

9. Idan kai da maƙwabcinka kun saɓa, ku daidaita a tsakaninku, kada a tona asiri.

10. Mai yiwuwa ne wani ya ji ya zarge ku, ba za ku taɓa rabuwa da wannan kunya ba.

11. Manufar da aka bayyana sosai kamar zubin zinariya take wanda aka yi a kan azurfa.

12. Faɗakarwar da mutumin da ya gogu da al'amuran duniya ya yi ga wanda yake da niyya ya kasa kunne, tamaninta ya fi na zoben zinariya, ko kayan ado da aka yi da zinariya tsantsa.