Littafi Mai Tsarki

K. Mag 16:24-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Kalmomi masu daɗi suna kama da zuma, suna da daɗin ɗanɗana, suna kuma da amfani domin lafiyarka.

25. Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.

26. Marmarin cin abinci yakan sa ɗan ƙodago ya yi aiki da ƙwazo, domin yana so ya ci ya ƙoshi.

27. Mutumin da yake jin daɗin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa ƙuna suke kamar wuta.

28. Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai.

29. Mutum mai ta da zaune tsaye yakan ruɗi abokansa, ya kai su ga bala'i.

30. Ka kula da mutane masu murguɗa baki suna kaɗa gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan.

31. Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.

32. Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

33. Mutane sukan jefa kuri'a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake ba da amsa.