Littafi Mai Tsarki

K. Mag 1:22-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ta ce, “Wawayen mutane! Har yaushe za ku yi ta kasancewa haka? Har yaushe za ku daina jin daɗin yi wa mai ilimi ba'a? Faufau ba za ku taɓa koya ba?

23. Ku kasa kunne lokacin da nake tsauta muku, zan ba ku shawara mai kyau, mu yi tarayya cikin ilimina.

24. Ina ta kiranku ina gayyatarku ku zo, amma ba ku kula ba, ba ku mai da hankali gare ni ba.

25. Kun ƙi bin shawarwarina duka, ba ku yarda in gyara kuskurenku ba.

26. Saboda haka, lokacin da kuke shan wahala, zan yi muku dariya. Zan yi muku ba'a lokacin da razana ta auka muku,

27. sa'ad da ta zo muku kamar hadiri mai ƙaƙƙarfar iska mai wahalarwa, sa'ad da kuke shan azaba da damuwa.

28. Sa'an nan za ku kira gare ni, amma ba za ku same ni ba. Za ku neme ni a ko'ina, amma ba za ku same ni ba.