Littafi Mai Tsarki

Fit 5:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai suka ce, “Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi.”

4. Amma Sarkin Masar ya ce wa Musa da Haruna, “Me ya sa kuke hana jama'ar yin aikinsu? Ku tafi wurin aikin gandunku.”

5. Ya kuwa ci gaba ya ce, “Ga jama'ar ƙasar sun yi yawa, yanzu kuna so ku hana su yin aikinsu.”

6. A ran nan fa Fir'auna ya umarci shugbannin aikin gandu da manyan jama'a, ya ce,

7. “Nan gaba kada ku ƙara ba mutanen nan budu na yin tubali kamar dā. Ku sa su, su tafi, su tara budu da kansu.

8. Duk da haka, kada su kāsa cika yawan tubalin da aka ƙayyade musu da fari. Ai, su ragwaye ne, shi ya sa suke kuka, suna cewa, ‘A bar mu, mu tafi mu miƙa wa Allahnmu hadaya.’

9. Ku sa mutanen su yi aiki mai tsanani har da ba za su sami damar kasa kunne ga maganganun ƙarya ba.”

10. Sai shugabannin aikin gandu da manyan jama'a suka tafi suka faɗa wa jama'a cewa, “Ga abin da Fir'auna ya ce, ‘Ba zan ba ku budu ba.

11. Ku je, ku da kanku, ku nemi budu inda duk za ku iya samowa, amma daɗai, ba za a sawwaƙe muku aikinku ba.”’

12. Sai jama'a suka watsu ko'ina cikin ƙasar Masar, suna tattara budu.

13. Shugabannin aikin gandun suka matsa musu, suna cewa, “Sai ku cika aikinku na kowace rana daidai yadda kuke yi a dā lokacin da ake ba ku budu.”

14. Aka kuwa bulali manya waɗanda suke Isra'ilawa waɗanda shugabannin aikin gandu na Fir'auna suka sa a bisa Isra'ilawa, ana cewa, “Me ya sa jiya da yau ba ku cika yawan tubalin da aka ƙayyade, kamar dā ba?”

15. Manyan Isra'ilawa kuwa suka tafi suka yi kuka a gaban Fir'auna, suka ce, “Me ya sa ka yi wa bayinka haka?