Littafi Mai Tsarki

Fit 40:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada,

7. ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ka zuba ruwa a ciki.

8. Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa'an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar.