Littafi Mai Tsarki

Fit 40:3-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule.

4. Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa.

5. Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa.

6. Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada,

7. ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ka zuba ruwa a ciki.

8. Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa'an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar.

9. “Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa alfarwa da dukan abin da yake cikinta, domin ka tsarkake ta da kayayyakinta duka, za ta kuwa zama tsarkakakkiya.

10. Ka shafa wa bagade na ƙona hadaya da kayayyakinsa duka man domin ka tsarkake shi, bagaden kuma zai zama mafi tsarki.

11. Ka kuma shafa wa daron da gammonsa man keɓewa, da haka za ka tsarkake shi.

12. “Ka kuma kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwa ta sujada, ka yi musu wanka da ruwa.

13. Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist.

14. Sai ka kawo 'ya'yan Haruna maza, ka kuma sa musu taguwoyi.

15. Sa'an nan ka shafa musu mai kamar yadda ka shafa wa mahaifinsu domin su yi mini aiki a matsayin firistoci. Shafa musu man zai sa su zama firistoci din din din dukan zamanansu.”

16. Haka kuwa Musa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.