Littafi Mai Tsarki

Fit 40:17-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. A rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu, aka kafa alfarwa.

18. Sai musa ya kafa alfarwa, ya kafa kwasfanta, ya jera katakanta, ya sa mata sandunanta, ya kakkafa dirkokinta.

19. Sa'an nan ya shimfiɗa murfi a bisa alfarwa ya rufe alfarwar kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

20. Sai ya ɗauki dokoki goma ɗin, ya sa a akwatin, ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin a bisansa.

21. Ya kawo akwatin a cikin alfarwa, sa'an nan ya sa labulen don kāre akwatin alkawari, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

22. Musa ya sa teburin cikin alfarwa ta sujada, a wajen gefen arewa na alfarwa, a gaban labulen.

23. Sa'an nan ya jera gurasa daki-daki a bisa teburin a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

24. Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa.

25. Ya kunna fitilun a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

26. Ya kuma sa bagade na zinariya a cikin alfarwa ta sujada daga gaban labulen.

27. Sai ya ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

28. Ya sa labule a ƙofar alfarwa.