Littafi Mai Tsarki

Fit 39:33-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Sai suka kawo wa Musa alfarwa da dukan kayayyakinta, wato da maratayanta, da katakanta, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

34. da murfi na fatun raguna da na awaki, da labulen,

35. da akwatin alkawari da sandunansa, da murfinsa,

36. da tebur, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,

37. da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,

38. da bagade na zinariya, da man keɓewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar alfarwar,

39. da bagade na tagulla da ragarsa ta tagulla, da sandunansa da dukan kayayyakinsa, da daro da gammonsa,

40. da labulen farfajiya da dirkokinta, da kwasfanta, da labulen ƙofarta, da igiyoyinta, da turakunta, da dukan kayayyakin yin aiki a alfarwa ta sujada,

41. da tufafin ado na aiki a Wuri Mai Tsarki, wato tsarkakan tufafin Haruna firist, da tufafin 'ya'yansa maza don su yi aikin firistoci.

42. Isra'ilawa sun yi dukan aiki kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

43. Da Musa ya duba dukan aikin, ga shi kuwa, sun yi shi daidai, kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Musa ya sa musu albarka.