Littafi Mai Tsarki

Fit 39:29-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Sun kuma yi abin ɗamara da lallausan lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi mata ɗinkin ado kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

30. Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, “MAI TSARKI GA UBANGIJI.”

31. Suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

32. Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra'ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

33. Sai suka kawo wa Musa alfarwa da dukan kayayyakinta, wato da maratayanta, da katakanta, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

34. da murfi na fatun raguna da na awaki, da labulen,

35. da akwatin alkawari da sandunansa, da murfinsa,

36. da tebur, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,

37. da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,