Littafi Mai Tsarki

Fit 38:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ya sa ƙawane huɗu a kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sanduna.

6. Ya kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ya dalaye su da tagulla.

7. Sai ya zura sandunan cikin ƙawane na gyaffan bagaden don ɗaukarsa. Ya yi bagaden da itace sa'an nan ya robe cikinsa.

8. Ya yi daron wanka da tagulla, da gammonsa na tagulla, daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.

9. Ya kuma yi farfajiya. Ya yi labulenta na gefen kudu da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne.

10. Da tagulla aka yi dirkokinsa ashirin, da kwasfan dirkoki guda ashirin, amma da azurfa aka yi maratayan dirkoki da maɗaurai.

11. Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne. An yi dirkokinsa guda ashirin da kwasfansu ashirin da tagulla, amma an yi maratayan dirkoki da maɗaurai da azurfa.

12. Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne, da kwasfansu guda goma. An yi maratayan dirkoki, da maɗaurai da azurfa.

13. Tsawon gefen gabas kamu hamsin ne.