Littafi Mai Tsarki

Fit 28:34-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Za a jera su bi da bi, wato 'ya'yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya.

35. Sai Haruna ya sa taguwar sa'ad da yake aiki. Za a ji ƙarar ƙararrawar a lokacin da yake shiga da lokacin da yake fita Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji don kada ya mutu.

36. “Sai kuma a yi allo na zinariya tsantsa, a zana rubutu irin na hatimi a kansa haka, ‘MAI TSARKI GA UBANGIJI.’

37. Sai a ɗaura shi da shuɗiyar igiya a rawanin daga gaba.

38. Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra'ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji.

39. “Ku saƙa zilaika da lallausan zaren lilin. Ku yi rawani da lallausan zaren lilin, ku kuma saƙa abin ɗamara mai ado.

40. “Za a yi wa 'ya'yan Haruna, maza, zilaiku, da abubuwan ɗamara, da huluna don daraja da kwarjini.

41. Ka sa wa Haruna, ɗan'uwanka, da 'ya'yansa maza, sa'an nan ka zuba musu mai, ka keɓe su, ka tsarkake su domin su zama firistoci masu yi mini aiki.

42. Sai kuma ku yi musu mukurai na lilin don su rufe tsiraicinsu daga kwankwaso zuwa cinya.

43. Haruna da 'ya'yansa maza za su sa su sa'ad da suke shiga alfarwa ta sujada ko kuwa sa'ad da suka kusaci bagade domin su yi aiki cikin Wuri Mai Tsarki domin kada su yi laifin da zai zama sanadin mutuwarsu. Wannan zai zama doka ga Haruna da zuriyarsa har abada.”