Littafi Mai Tsarki

Fit 28:32-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Za a yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A yi wa wuyan shafi, sa'an nan a yi wa wuyan basitsa, wato cin wuya, domin kada ya kece.

33. Za a yi wa karbun taguwar ado da fasalin 'ya'yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu.

34. Za a jera su bi da bi, wato 'ya'yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya.

35. Sai Haruna ya sa taguwar sa'ad da yake aiki. Za a ji ƙarar ƙararrawar a lokacin da yake shiga da lokacin da yake fita Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji don kada ya mutu.

36. “Sai kuma a yi allo na zinariya tsantsa, a zana rubutu irin na hatimi a kansa haka, ‘MAI TSARKI GA UBANGIJI.’

37. Sai a ɗaura shi da shuɗiyar igiya a rawanin daga gaba.

38. Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra'ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji.

39. “Ku saƙa zilaika da lallausan zaren lilin. Ku yi rawani da lallausan zaren lilin, ku kuma saƙa abin ɗamara mai ado.

40. “Za a yi wa 'ya'yan Haruna, maza, zilaiku, da abubuwan ɗamara, da huluna don daraja da kwarjini.