Littafi Mai Tsarki

Fit 28:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Za a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a bisa duwatsun nan kamar yadda mai yin aiki da lu'ulu'u yakan zana hatimai. Za a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya.

12. A sa duwatsun a kafaɗun falmaran domin a riƙa tunawa da 'ya'yan Isra'ila. Haruna zai rataya sunayensu a kafaɗunsa a gaban Ubangiji domin a tuna da su.

13. Za ku yi tsaiko biyu na zinariya,

14. ku kuma yi tukakkun sarƙoki biyu na zinariya tsantsa. Za ku ɗaura wa tsaikunan nan tukakkun sarƙoƙi.

15. “Ku kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji domin neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa falmaran ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.

16. Ƙyallen maƙalawa a ƙirji zai zama murabba'i, a ninke shi biyu tsawonsa da fāɗinsa su zama kamu ɗaya ɗaya.

17. Sai a yi jeri huɗu na duwatsun a kanta. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.

18. A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon.