Littafi Mai Tsarki

Fit 25:31-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. “Ku kuma yi alkuki da zinariya tsantsa. Ku yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙuna, da mahaɗai, da furanninsa a haɗe da shi za ku yi su.

32. Alkukin ya kasance da rassa shida, rassa uku a kowane gefe.

33. A kowane reshe na alkuki za a yi ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond. Ya kasance kuma da mahaɗai da furanni.

34. Za a yi wa gorar alkukin ƙoƙuna huɗu masu kamar tohon almond, da mahaɗai da furanni.

35. A gindin kowane reshe biyu za a yi mahaɗi ɗaya.

36. Da mahaɗai da rassan za su kasance a haɗe da alkukin. Da ƙerarriyar zinariya za a yi su.

37. Ku kuma yi fitilu bakwai, ku sa su a bisa alkukin ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.

38. Ku kuma yi hantsuka da farantai da zinariya tsantsa.

39. Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya za ku yi alkukin da waɗannan abubuwa duka.

40. Sai ku lura, ku yi waɗannan abubuwa duka bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.”