Littafi Mai Tsarki

Fit 25:31-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. “Ku kuma yi alkuki da zinariya tsantsa. Ku yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙuna, da mahaɗai, da furanninsa a haɗe da shi za ku yi su.

32. Alkukin ya kasance da rassa shida, rassa uku a kowane gefe.

33. A kowane reshe na alkuki za a yi ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond. Ya kasance kuma da mahaɗai da furanni.

34. Za a yi wa gorar alkukin ƙoƙuna huɗu masu kamar tohon almond, da mahaɗai da furanni.

35. A gindin kowane reshe biyu za a yi mahaɗi ɗaya.

36. Da mahaɗai da rassan za su kasance a haɗe da alkukin. Da ƙerarriyar zinariya za a yi su.

37. Ku kuma yi fitilu bakwai, ku sa su a bisa alkukin ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.