Littafi Mai Tsarki

Fit 21:33-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. “Idan mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai rufe ba, in sa ko jaki ya fāɗa ciki,

34. mai ramin zai biya mai san ko mai jakin, mushen ya zama nasa.

35. Idan san wani ya yi wa na wani rauni har ya mutu, sai ya sayar da san da yake da rai a raba kuɗin. Haka kuma za su raba mushen.

36. Amma idan dā ma an sani san mafaɗaci ne, mai san kuwa bai kula da shi ba, sai ya biya, wato ya ba da sa a maimakon mushen. Mushen kuwa zai zama nasa.”