Littafi Mai Tsarki

Fit 12:35-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Isra'ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi.

36. Ubangiji ya sa jama'a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.

37. Isra'ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot.

38. Babban taron tattarmuka kuma suka tafi tare da su, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu tinjim.

39. Suka toya abinci marar yisti da ƙullun da suka fita da shi daga Masar, gama ba su sa yisti cikin ƙullun ba domin an iza ƙyeyarsu, ba su sami damar dakatawa ba, ba su kuwa shirya wa kansu guzuri ba.

40. Zaman da Isra'ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin.

41. A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.

42. Daren nan da Ubangiji ya sa domin ya fito da Isra'ilawa daga ƙasar Masar, daren ne wanda wajibi ne Isra'ilwa su kiyaye domin su girmama Ubangiji dukan zamanansu.

43. Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Wannan ita ce ƙa'idar Idin Ƙetarewa, baƙo ba zai ci ba.

44. Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya.

45. Amma da baƙo da wanda aka yi ijararsa ba zai ci shi ba.

46. A gidan da aka shirya, nan za a ci, kada a fitar da naman waje, kada kuma a karye ƙashinsa.

47. Dukan taron jama'ar Isra'ila za su kiyaye Idin Ƙetarewa.