Littafi Mai Tsarki

Esta 8:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A wannan rana sai sarki Ahasurus ya ba Esta gidan Haman, maƙiyin Yahudawa, da duk dukiyar Haman. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, gama Esta ta bayyana yadda yake a gare ta.

2. Sa'an nan sarki ya ɗauki zobensa na hatimi, wanda ya karɓe a wurin Haman, ya ba Mordekai. Esta kuma ta ba Mordekai gidan Haman.

3. Sa'an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roƙe shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba'agage ya shirya wa Yahudawa.

4. Sai sarki ya miƙo wa Esta sandan sarauta na zinariya.

5. Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, “Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba'agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da suke cikin dukan lardunan sarki.

6. Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da hallaka na mutanena da dangina?”

7. Sai sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya da Mordekai, Bayahude, “Ga shi, na riga na ba Esta gidan Haman, an kuma riga an rataye shi a bisa gungume domin ya so ya taɓa Yahudawa.